Buhari da tsofaffin shugabannin kasa sun bukaci ‘yan takara su amince da sakamakon zabe

0
53

Gabanin zaben 2023, shugaban kasa Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon (rtd), tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, da tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd), sun bukaci dukkan ‘yan takarar a mukamai daban-daban da su mutunta zabin ‘yan kasa masu kada kuri’a kuma su amince da sakamakon zaben kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana.

Buhari, wanda ya yi magana a ranar Laraba a Abuja a wajen rattaba hannu na biyu na yarjejeniyar zaman lafiya da jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar shugaban kasa suka yi, wanda kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) ya shirya, ya kuma bukaci duk wani dan takara da bai gamsu da sakamakon zaben ba da ya garzaya kotu domin bin tsarin shari’ar kasar.

Mambobin kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin jagorancin Janar Abdusalami Abubakar, da shugaba Buhari, da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Janar Yakubu Gowon, da sauran manyan baki ne suka halarci taron.

Daga cikin ‘yan takarar da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar akwai Bola Tinubu na jam’iyyar APC, Peter Obi na jam’iyyar Lebo (LP), Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here