Sumamen da DSS ta kai ofishin NNPP a Kano ya bar baya da kura

0
118

Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta zargi hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da razanar da mambobinta tare da kai samame a ofisoshin yakin neman zabenta a jihar.

Sai dai hukumar DSS, a cikin martanin da ta mayar cikin gaggawa, ta ce, bata wariya wajen gudanar da ayyukanta, kuma ta bai wa dukkanin jam’iyyun siyasa dama iri daya, inda ta ce kawai ta kwato muggan makamai ne daga ofisoshin yakin neman zabe na wasu ‘yan siyasa.

Wannan zargi na babbar jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar, ya zo ne kwanaki kadan bayan da jam’iyyar ta zargi shugabannin ‘yan sanda a jihar da hada kai da gwamnatin jihar wajen muzgunawa mambobinta da kame su.

Daily trust ta ruwaito cewa, babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya, Usman Baba, ya mayar da kwamishinan ‘yan sandan jihar zuwa jihar Filato tare da sanya sabbin jami’an kwamishinonin ‘yansanda guda biyu da mataimaka 3 da za su kula da jihar a lokacin zaben.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Larabar da ta gabata, shugaban NNPP na jihar, Umar Haruna Doguwa, ya yi zargin cewa wasu jami’an DSS sun kai wani samame a ofisoshin daraktan kungiyoyi magoya bayan jam’iyyar NNPP da na daraktan tattarowa da wayar da kan matasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here