Yayin da ‘yau Najeriya ke gudanar da zaben shugaban kasa tun bayan dawowar wannan tafiyar dimokiradiyar a shekarar 1999, wannan itace dama ta 3 da za’a samu sauyin gwamnati daga shugaban kasa mai barin gado zuwa wani sabon shugaban kasa.
Abin nufi anan shine mika mulki daga shugaba Olusegun Obasanjo zuwa shugaba Umaru Musa Yar’Adua shine karo na farko da aka samu sauyin gwamnati tsakanin shugaba mai barin gado da kuma wanda ya lashe zabe.
Bayan wannan sai sauya gwamnatin da aka samu tsakanin shugaba Goodluck Jonathan wanda ya gaji Yar’Adua zuwa shugaba Muhammadu Buhari wanda ke kawo karshen mulkinsa a watan Mayu mai zuwa.
Bayan zaben na yau ana saran shugaba Muhammadu Buhari ya mika ragamar tafiyar da kasar ga ‘dan takarar da zai samu nasara tsakanin Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar da Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, ko kuma sauran ‘yan takara 14 dake fafatawa a zaben mafi girma da za’a gani saboda yawan masu kada kuri’u.
Masana siyasar duniya na bayyana cewar a irin wannan lokacin da ake gudanar da zabukan sauya gwamnati akan samu matsaloli a kasashe masu tasowa, musamman irin na Afirka abinda ke haifar da tashe tashen hankula.
Sai dai masu nazari da dama na ci gaba da yaba yadda hukumar zaben Najeriya ke inganta ayyukan ta daga zabe zuwa wani zaben, musamman wajen bijiro da sabbin na’urorin zamani wadanda ke taimaka musu wajen kawar da magudi.