Zaben 2023: ICPC ta damke wani mutum da sabbin kudi na miliyan 2 a Bauchi

0
57

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), ta kama wani mutum dauke da tsofaffin takardun kudi na Naira miliyan biyu da kuma sabbin takardun kudi na Naira miliyan biyu a karamar hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.

Wanda ake zargin, Hassan Ahmad, an kama shi ne a ranar Juma’a da kudin a cikin jakar ‘Ghana Must Go’ a lokacin da yake tuka wata mota kirar Hilux.

An kama shi yana kan hanyarsa ta zuwa Gombe daga jihar Bauchi.

Ana zargin zai kai wa wani dan siyasa kudin.

ICPC ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.

“Ofishin ICPC na Jihar Bauchi ya kama wani Hassan Ahmad da tsofaffin takardun kudi Naira miliyan biyu da kuma sabbin kudi a cikin halin kuncin da ake ciki a kasar nan.

“Rundunar sojin da aka tura Alkaleri a Jihar Bauchi sun kama wanda ake zargin ne a ranar Juma’a, kuma sun mika shi ga ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Bauchi.

“Ahmad ya mallaki tsabar sabbin kudi N900,000 da kuma Naira miliyan 1.1 na tsofaffin kudi a wata mota kirar Hilux bakar fata mai lamba JMA 85 AZ.

“Kudin na cikin jakar ‘Ghana Must Go’.

“Wanda ake zargin ya amsa cewa zai kai kudaden ne Jihar Gombe ga wani dan siyasa don raba su a ranar zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here