Zaben 2023: INEC ta sanar da ranar da za’a fara tattara sakamakon zaben shugaban kasa

0
117

A ranar Lahadi ne za a fara tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar, kamar yadda shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar.

Yakubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan yadda zaben ya gudana a fadin kasar ranar Asabar.

Shugaban na INEC ya ce tsarin tantance masu kada kuri’a na (BVAS) ya yi aiki yadda yakata a yawancin jihohin kasar nan, amma hukumar ta fuskanci kalubale a wasu sassan kasar.

Yakubu ya kara da cewa kalubalen da ake fuskanta shi ne gazawar hukumar na bude rumfunan zabe da karfe 8:30 na safe kamar yadda aka tsara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here