Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ’yan daba sun tarwatsa wuraren zabe tare da da sace na’urar tantance masu zabe (BVAS) guda takwas a jihohin Delta da Katsina.
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa ’yan daba sun kwace na’urar BVAS guda shida a wani hari da suka kai rumfar zabe a Karamar Hukumar Safana a Jihar Katsina, inda suka yi.
An kai makamancin harin a Karamar Hukumar Oshimili a Jihar Delta, inda sauka yi awon gaba da na’urar BVAS guda biyu.
Ta sanar da haka ne a ranar Asabar yayin da yake jawabi game da zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisar Tarayya da ke gudana.
Yakubu ya koka kan cewa, bayyane yake bata-garin sun maida hankalinsu ne kan na’urorin BVAS da ake amfani da su a wannan zabe.
Ya ce, ”Muna ba da tabbacin za mu ci gaba da yin abin da shi ne daidai, shi ya sa muka zabi yi wa ’yan kasa bayani a daidai wannan gabar, kuma za mu ci gaba da yin haka.
Ya ce hakki ne da ya rataya a wuyan INEC tabbatar da sahihin zabe a kasa.