Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Kano

0
77

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP ya lashe zaben shugaban kasa a Jihar Kano.

Kwakwaso ya yi nasara ne bayan ya samu gagarumin rinjaye a manyan ’yan takarar shugaban kasa da suka hakda da Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP, Bola Tinubu na APC, da kuma Peter Obi na LP a zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 a Jihar Kano

Kwankwaso ya samu kuri’u 997,278 inda ya doke Tinubu da ya zo a na biyu da kuri’u 517,341, sai Atiku na jam’iyyar PDP da kuri’u 131,604.

Sai Peter Obi na jam’iyyar LP da ya kare da kuri’u 28,522.

Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan Kano je har sau biyu, ya lashe kananan hukumomi 36 daga 44 da ke jihar, yayin da Tinubu ya lashe ragowar kananan hukumomi takwas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here