Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Bola Tinubu ya doke Atiku Abubakar, Peter Obi da kuma Rabi’u Musa Kwankwaso a zaben shugaban kasa a Jihar Neja.
Tinubu ya lashe kananan hukumomi 21 cikin 25 yayin da Atiku Abubakar ya lashe kananan hukumomi uku, sai Peter Obi na jam’iyyar LP da ya samu nasara a karamar hukumar Suleja.
Da yake bayyana sakamakon zaben, jami’in tattara bayanai na jihar Neja kuma mataimakin shugaban Jami’ar Abuja, Farfesa Clement Allawa, ya ce APC ta samu kuri’u 375,183 yayin da PDP ta samu kuri’u 284,898.
Kazalika, ya ce jam’iyyar LP ta samu kuri’u 80,452 yayin da jam’iyyar NNPP ta samu kuri’u 21,836.
Sai dai Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja ya lashe kujerar Sanatan Neja ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC.
Bello ya zo na daya, inda ya doke dan takarar jam’iyyar PDP wanda ya zo na biyu.
Da yake bayyana sakamakon zaben a garin Kontagora, jami’in zaben, Farfesa Kolo Zacchaeus, ya ce Abubakar Sani Bello, ya samu kuri’u 100,197 inda ya doke ‘yan takarar jam’iyyar PDP, Shehu Muhammad Abdullahi wanda ya samu kuri’u 88,153 da dan takarar jam’iyyar NNPP, Ibrahim Wali wanda ya samu kuri’u 13, 886.