Atiku ya lashe zabe a Kebbi

0
109

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa ya lashe zaben shugaban kasa a Jihar Kebbi.

Gwamnan Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, shi ne kodinetan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu.

Baturen zaben shugaban kasa a Jihar Kebbi, Farfesa Yusuf Sa’idu ya ce Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP ya yi nasara da kiri”u 288,175.

Na biye da shi shi ne Bola Tinubu na APC mai kuri’u 248,088.

Peter Obi na LP ya zo na uku da kuri’a 10,682, sai Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya zo na hudu da kuri’a 5,038.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here