Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Tinubu

0
61

A safiyar ranar Laraba ne INEC ta sanar da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Tinubu ya kayar da Atiku wanda ya zo na biyu, sai Peter Obi da ya zo a na ukuz sai Rabiu Musa Kwankwaso da ya kare a na hudu.

Amma akwai wasu abubuwa guda biyar da ya kamata ku sani game da sabon angon Nijeriya.

1. Bai taba faduwa zabe ba: Sabon shugaban kasar Nijeriya, Tinubu yana da tarihin bai taba faduwa takara ba tun da ya fara siyasa. Wannan na da nasaba da idan aka yi duba da mukaman da ya rike a baya.

2. Tinubu ya fara takara a jam’iyyar SDP a shekarar 1992.

3. Ya yi gwamnan Jihar Legas sau biyu a jera daga 1999 zuwa 2007.

4. Tinubu ya samu digiri a Jami’ar Chicago da ke Amurka a 1979 a bangaren (Accounting).

5. Tinubu ya kasance dan kasuwa. Baya ga siyasa sabon shugaban kasae fitaccen dan kasuwa ne a bangaren gina gidaje, harkar danyen mai kuma shi ne shugaban kamfanin Alpha Beta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here