DA DUMI-DUMI: INEC ta ayyana dukkan zabukan ‘yan majalisar dokokin jihar Sokoto a matsayin wanda bai kammala ba

0
105

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INCE) ta bayyana cewa duk zabukan ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar Sokoto ba su kammalu ba.

Kakakin hukumar a jihar, Dr. Shamsuddeen Haliru ne ya bayyana hakan a ranar Laraba 1 ga Maris, 2023.

Ya ce, “ Dukkan mazabu na tarayya 11 da kuma gundumomin Sanata uku na jihar ba’ayyana wanda yaci zabe ba don haka, za’a kara saka lokacin yin  zaɓe .”

A cewar jaridar PUNCH, an samu rudani dangane da jinkirin da aka samu na bayyana sakamakon zaben majalisar dokokin jihar, inda magoya bayan manyan jam’iyyun siyasar biyu suka yi ta yada sakamakon bogi a shafukan sada zumunta na yanar gizo, domin nuna goyon baya ga jam’iyyunsu.

A cikin wadannan rahotannin na karya, ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasa biyu na jihar, PDP da APC ne ke kan gaba a bangarori daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here