Lokaci ya yi da zan sanya kowa farin ciki a Najeriya — Tinubu

0
108

Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa bayan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ayyana shi a matsayin zababben shugaban kasar Nijeriya da safiyar Laraba.

“Na yi matukar kaskantar da kai don yin aiki a matsayin shugaban kasa na 16. “Wannan lokaci ne mai haske a rayuwar kowane mutum kuma zan tabbatar da wanzuwar dimokuradiyyarmu, “in ji shi.

Tsohon gwamnan Jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya nuna godiyarsa ga dukkan wadanda suka halarci zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

“Ina amfani da wannan damar wajen yin kira ga ’yan uwana masu takara da su zo mu tare. Ita ce kawai al’ummar da muke da ita. Kasa daya ce kuma dole ne mu gina tare,” in ji shi.

Tinubu, mai shekaru 70, ya zo kan gaba a jihohi 12 daga cikin 36 na Nijeriya, kuma ya samu kuri’u masu yawa a wasu jihohi da dama, inda ya samu kuri’u mafi yawa – miliyan 8,794,726, kusan kuri’u miliyan biyu ya zarce mai biye masa – tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Abubakar mai shekaru 76, wanda yanzu ya tsaya takarar shugaban kasa sau shida, ya samu kuri’u 6,984,520, yayin da dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, wanda bai kai shekara guda da fara takara ba, ya samu kuri’u 6,101,533.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here