Buhari ba ya mutunta bangaren shari’a – Kotun Koli

0
51
Kotun Kolin Najeriya ta ce, shugaban kasar, Muhammadu Buhari baya mutunta bangaren shari’a, yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin kotun kolin da kuma bangaren zartaswa.
Kotun mai mambobi bakwai karkashin jagorancin John Okoro, ta bayyana hakan ne bayan zaman hukuncin korafin da wasu gwamnonin kasar suka shigar mata, kan sauya wasu takardun kudin kasar da babban bankin CBN ya yi.

Guda daga cikin alkalan, Emmanuel Agim, ya ce rashin mutunta umarnin kotun da shugaban ya yi, daidai yake da gazawar kundin tsarin mulki da kuma mulkin dimokradiyya, inda yanzu aka maye gurbinsu da tsarin kama karya.

An kai ruwa rana tsakanin kotun kolin Najeriya da kuma bangaren zartaswa, game da batun sabunta kudin kasa, kasancewar duk da umarnin kotun na sahalewa a cigaba da amfani da kudaden da CBN ta ce an daina, hakan ya haifar da rudani a tsakanin ‘yan kasar.

An yi zargin cewa CBN ya gaza buga sabbin takardun kudi ta yadda za su wadatar da ‘yan Najeriya, lamarin da ya jefa su cikin mummunan yanayi.

Shirin sabunta takardun kudi, wanda shugaba Buhari ya bayar da umarni ya haifar da karancin kudi a sassan. kasar, abin da ya haifar da matsin tattalin arziki, musamman ga masu karamin karfi da kananun ‘yan kasuwa.

Gwamnoni uku ne dai, wato na jihohin Kaduna, Kogi da kuma Zamfara ne suka gurfanar da gwamnatin tarayyar gaban kotun kolin, suna mika bukatar a tsawaita wa’adiin da gwamnati ta bawa ‘yan kasar.

Amma a wani abu da ake ganin ya keta dokokin Kotun, ranar 16 ga watan Fabrairu, shugaba Buhari, yayin wani jawabi da ya gabatarwa ‘yan kasar, y ace za a ci gaba da amfani da takardun kudi na naira 200 ne kawai daga cikin takardun kudin da aka sabunta.

 

Mista Agim ya ce, “Sanarwar shugaban na amfani da takardar kud na naira 200, tabbas rashin da’a ne karara ga umarnin.

Buhari, wanda ya mulki Najeriya karkashin mulkin soja a shekarun 1980, an sake zaben sa a mulkin Dimokradiyya a shekara ta 2015.

Amma tun daga lokacin da ya karbi mulkin kasar a karo na biyu, ana ganin shugaban ya gaza cika wasu alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.

Jawabin kotun na ranar Juma’a, shi ne karo na farko da bangaren shari’a ya nuna wa shugaban yatsa a matsayin sa na wanda ya kasa mutunta umarni daga bangaren shari’a.

(rfi)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here