Abin Al-ajabi: Yadda likitocin Madina suka farfado da wani mahajjaci bayan ya daina numfashi

0
88

Cikin bada agajin gaggawa daga jami’an lafiya na Masallacin Harami na Madina, an yi nasarar ceto rayuwar wani alhajin Umrah, ɗan kasar Pakistan, wanda zuciyarsa ta daina aiki tsawon sama da mintuna 10 a Masallacin Annabi da ke Madina.

Tawagar likitocin sun samu sanarwar gaggawa don tunkarar wani majinyaci mai shekaru 70 da ke fama da matsalar lafiya, wanda ya fita daga hayyacinsa a cikin harabar masallacin Annabi (SAW).

Yayin da motar ɗaukar mara lafiya ta garzayo wajen da gaggawa, an samu nasarar ceto alhajin, in da kuma aka gano cewa majinyacin cewa na fama da ciwon zuciya da wahalar numfashi.

Tawagar likitocin nan take ta fara yi masa gwajin CPR tare da sauran gwaje-gwaje na tsawon sama da mintuna 10 har sai da zuciyar ta sa ta ci gaba da bugawa.

Daga nan aka mayar da majiyyacin zuwa cibiyar lafiya ta Al-Safiah don kammala shirin jinya, sannan aka ba shi magungunan da suka dace har sai da lafiyarsa ta kwanta ya bar cibiyar.

Abin lura ne cewa Cibiyar Al-Safiah ta karbi waɗanda zuciyar su ta daina aiki har sau 7 da cututtukan numfashi guda 48, da bugun zuciya guda takwas a harabar masallacin Annabi (SAW) tun farkon wannan shekarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here