‘Yan sanda sun kashe masu garkuwa 2 da ceto mutum 1 a Bauchi

0
29

Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta samu nasarar hallaka wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan garkuwa da mutane ne sa’ilin da suka yi yunkurin garkuwa da wani mutum mai suna Usman Abdulhamid.

A wata sanarwar manema labarai da kakakin hukumar, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar tare da raba wa ‘yan jarida a Bauchi ranar Lahadi, ya shaida cewar a bisa kokarinsu da himmarsu na dakile ta’addanci ne suka samu wannan nasarar.

Ya ce, a ranar 3 ga watan Maris wasu ‘yan bindiga suka mamaye gidan Alhaji Abdulhamid Muhammad da ke kauyen Rafin Cora a karamar hukumar Ningi domin su yi garkuwa da dansa mai suna Usman Abdulhamid dan shekara 28 a duniya.

A kan hakan, shi Usman ya jajirce tare da tirjijewa, lamarin da har sai da ta kai masu garkuwan sun bude masa ruwan harsasai a cikinsa a lokacin da ya yi kokarin guje musu.

 

Wakil ya kara da cewa, “Cikin hanzari daga samun rahoton faruwar lamarin, hadakar jami’an ‘yansanda da ‘yan Bijilante a karkashin jagorancin DPO din Ningi, inda suka nausa zuwa wajen da abun ya faru domin taka wa masu garkuwan burki. Amma isarsu ke da wuya ‘yan garkuwa suka marabcesu da harbe-harbe.”

A matsayin maida martani, ‘yansandan su ma sun bude wuta ga masu garkuwan inda aka yi bata-kashi a tsakani.

Ya ce, “Bisa shan karfinsu da ‘yansanda suka yi, biyu daga cikin masu garkuwan sun mutu, an kuma kwato bindiga kirar AK47 guda daya a wajen da aka fafatan.”

 

Ya kara da cewa, an samu nasarar ceto wanda suka yi kokarin garkuwa da shi tare da kaisa zuwa asibitin gwamnatin tarayya da ke Birnin Kudu a jihar Jigawa domin nema masa kulawar likitoci.

 

“Tunin kuma aka dukufa wajen bin sawun masu garkuwa da mutanen domin tabbatar da an kamo su don su fuskanci shari’a,” Wakil din ya kara da fadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here