Gwamnatin Kaduna ta kammala shirye shiryen fara raba wasu shaguna na kasuwar Barci

0
90

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kammala shirye shiryen fara raba wasu shaguna na Kasuwar Barci da ke Tudun Wada da ta kammala gyaransu ga ’yan  kasuw.

Sai dai kuma wasu masu neman abinci a kasuwar sun koka a kan rashin kammala shagunan da ake shirin raba masu.

Gwamna Nasir El-Rufai ne dai ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa za a fara raba shagunan da aka kammala ginawa ga masu su a ranar Litinin mai zuwa.

Wallafa hotunan bangaren da aka kammala a shafin Gwamnan ya janyo ce-ce-ku-ce saboda rashin kammala ginin kasuwar.

Aminiya ta ziyarci kasuwar a ranar Juma’a, inda ta tarar da cewa har yanzu da sauran aikin domin kuwa kusan bangaren da aka yi wa alamar ‘A’ da ‘D’ ne kurum aka kammala.

Har yanzu akwai shaguna da ko rufi babu sannan wasu shagunan da aka kammala babu sili a cikinsu ballantana wutar lantarki.

Wasu daga cikin ’yan kasuwar sun yi fatan Allah Ya sa a basu shagunansu kamar yadda aka yi masu alkawari.

Gaskiya dai ginin kasuwar da sauran aiki domin za a iya cewa kila an kammala kashi 40 ne na kasuwar, ka ga kuwa akwai sauran aiki,” in ji wani mai sayar da takalma a gefen kasuwar.

Haka shi ma wani dan kasuwar wanda ya ki bayyana sunansa, ya ce “ba dai sun ce mu zo ranar Litinin ba za su fara raba shagunan, toh za mu zo mu na kuma fatan za a bai wa kowa shagonsa ba wai da an bai wa mutum uku a ce an tashi daga taro ba,” inji shi.

Shi kuwa wani mai suna Shehu mai sayar da kayan gwanjo cewa ya yi, “yadda kowa ya gani a yanar gizo haka muka ji.

“Kuma cewa aka yi wadanda suka biya kudin shago. Kenan kila ’yan siyasa kurum za a bai wa ba ainihin masu shagon ba,” inji shi.

Ita kuwa Shugabar Hukumar Kula da Ci gaban Kasuwanni ta jihar ta ce akalla akwai shaguna 1010 a sashen da za a rabar wato sashen ‘A’ da ‘D’ inda aka kammala.

“Akwai shago 1010 a bangaren ‘A’ da ‘D’ nan ne aka kammala kuma duk wadanda aka bai wa shago suna iya ci gaba da kasuwancin su kafin a kammala sauran bangaren kasuwar.

“Akwai hanyar shiga kasuwar da za a samar masu a yayin da kuma za a ci gaba da aikin sauran sashen kasuwar, shi ya sa muka tsaya kurum a bangaren ‘A’ da ‘D’, a yayin da ake ci gaba da sauran ayyuka” inji ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here