Kotun koli ta cire sunan Shekarau a matsayin zababben Sanatan Kano ta tsakiya

0
100

Kotun koli ta tabbatar da Rufai Hanga na jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP a matsayin zababben Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya.

Kotun kolin ta kuma cire tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim shekarau a matsayin dan takarar jam’iyyar NNPP a zaben majalisar dokokin kasar da a ka yi a yi ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kotun da ke yanke hukunci a karar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta shigar a gabanta, ta amince da hukuncin da babbar kotun tarayya da kotun daukaka kara da ke Abuja suka yanke, wadanda tun farko suka amince da takarar Rufai Hanga a matsayin dan takarar sanatan na  jam’iyyar.

A hukuncin da mai shari’a Uwani Aba-Aji ta shirya amma mai shari’a Emmanuel Agim ya gabatar, kotun kolin ta ce karar da hukumar ta INEC ta shigar ba ta da wani inganci kuma ta yi watsi da shi.

Babbar kotun tarayya da kotun daukaka kara a hukuncin da suka yanke a baya sun tabbatar da Rufa’i Hanga a matsayin dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP bayan ficewar Ibrahim Shekarau daga jam’iyyar kuma dan takarar Sanata saboda rashin jituwar da ake zargin ya samu da shi  jam’iyyar.

Maimakon yin biyayya ga umarnin babban kotun tarayya, INEC ta daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara kuma ta yi rashin nasara.

Hukumar ba ta gamsu da hukunce-hukuncen kotunan shari’a da daukaka kara ba, ta garzaya zuwa kotun koli don kalubalantar hukuncin da ta tabbatar da Rufai Hanga a matsayin halastaccen dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya na jam’iyyar NNPP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here