Real Madrid na shirin dauko Haaland daga Man City

0
88

Real Madrid na nazari a kan dauko dan wasan gaba na Manchester City a kaka mai zuwa, a kokarin da take na  kawo sabbin jini kungiyarta, wadanda suka hada da dan wasan tsakiya dan kasar Ingila, wanda ke wasa a Borussia Dortmund, Jude Bellingham.

Zakarun na naahiyar Turai sun yi amannar cewa sune ke kan gaba daga  cikin masu neman dan wasan gaban na Manchester UInited biyo bayan jerin tattaunawa da kungiyarsa.

Real Madrid din na kokarin dauko Haaland ne a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan gabanta, Karim Benzema mai shekaru 35.

Tun da farko Kylian Mbappe ne  Madrid suka yi niyyar daukowa, amma shawarsa ta ci gaba da zama a Paris Saint Germain ta janyo tankiya da rashin jituwa tsakaninsu, kuma hakan ya sa shugaban Madrid, Florentino Perez ya kudiri aniyar mayar da hankali a wani wuri.

Ana rade radin kocin Madrid  Carlo Ancelotti na iya  barin kungiyar a kaka mai zuwa, kuma hakan zai zo ne da sayen ‘yan wasan gaba da na tsakiya ciki har da Bellingham.

Tun da farko Perez ya yi niyyar dauko Haaland da Mbappe a lokaci guda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here