Shahararren dan kasuwar Kano ya rasu

0
231

Babban dan kasuwa kuma fitaccen dan kwangila a Jihar Kano, Alhaji Sani Dahiru Yakasai ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin dai shi ne nunin gine-gine na SDY, wanda yana daya daga cikin jiga-jigan kwangila a jihar da kewaye.

A cewar wata majiya, Alhaji Yakasai ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Majiyar ta kara da cewa, Yakasai ya rasu yana da shekaru 68 a duniya kuma ya bar matansa da ‘ya’yansa da jikoki.

An yi jana’izar sa a Kofar Kudu ta Fadar Sarkin Kano da misalin karfe 8 na safiyar wannan Juma’ar, sannan an binne gawarsa a makabartar Tarauni.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje; Sarkin Kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero da Sanata Ibrahim Shekarau, na daga cikin musulmin da suka halarci jana’izar dan kasuwan wadda ya rasu a jiya Alhamis.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here