Za a dage kidayar jama’a zuwa watan Mayu

0
84

Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta ce dage zaben Gwamnoni da na ’yan majalisun jihohi da aka yi da mako daya zai shafi jadawalinta na gudanar da kidayar jama’a na shekarar 2023.

A baya dai hukumar ta tsayar da ranakun 29 ga watan Maris zuwa biyu ga watan Afrilu a matsayin ranakun kidayar bayan shafe shekara 17 ba a kuma yin ta ba.

Wani jami’i a hukumar wanda bai amince a ambaci sunansa ba ne ya tsegunta wa Aminiya hakan, inda ya ce yanzu za a mayar da ranakun ne zuwa tsakanin uku da bakwai ga watan Mayun.

“A yanzu za a gudanar da kidayae tsakanin uku zuwa bakwai ga watan Mayu, shawara ce da aka aike wa Shugaban Kasa, kodayake ba a kai ga yanke ta ba tukunna,” in ji majiyar.

Shi ma Shugaban na NPC, Nasir Isa Kwarra, ranar Alhamis ya alamta cewa akwai yiwuwar a canza ranakun, lokacin da yake karbar wasu kayan tallafin kidayar daga Asusun Kula da Yawan Jama’a na Majalisar Dinkin Duniya (UNPFA) a Abuja.

Shugaban ya ce duk da ba a kai ga yanke shawarar ta karshe a kan lamarin ba, amma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne yake da cewa ta karshe a kan batun.

Daga nan sai ya yaba wa asusun saboda bayar da tallafin da kuma ci gaba da hadin gwiwa da hukumarsa.

A ranar Laraba ce dai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar da dage zaben daga ranar 11 zuwa 18 ga watan Maris, saboda ta sami zarafin sake saita na’urorin BVAS da za a yi zaben da su.

Bugu da kari, rabon da a ayi kidayar jama’a tun a shekara ta 2006.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here