MDD ta yi tir da kisan da mayakan ISWAP suka yi wa fararen hula a Borno

0
47

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da kisan fararen hula sama da 30 da wasu ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan kungiyar IS ne da ke yammacin Afirka wato ISWAP, suka yi a karamar hukumar Gamboru Ngala da ke jihar Borno.

Rahotanni sun tabbatar da cewa da dama daga cikin fararen hular da aka kashe masunta ne.

Wasu fararen hula da aka ce su ma sun sami raunuka daban-daban a yanzu haka ana kula da su a cibiyoyin lafiya.

Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Matthias Schmale, ya yi Allah-wadai da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta bayyana damuwa kan lamarin da ya faru a kauyen Mukdolo, da ke jihar Bornon.

Matthias Schmale ya ce har yanzu ba a san inda wasu fararen hular suka dosa ba, bayan harin da aka kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here