Neymar ya yi farin ciki bayan tiyatar da aka yi masa amma babu tabbas dangane da batun dawowarsa

0
137
FILE PHOTO: Soccer Football - Champions League - Round of 16 First Leg - Paris St Germain v Bayern Munich - Parc des Princes, Paris, France - February 14, 2023 Paris St Germain's Neymar reacts after sustaining an injury REUTERS/Christian Hartmann/File Photo

Likitoci har yanzu ba su da tabbacin lokacin da dan wasan gaban Brazil Neymar zai iya komawa taka leda ba duk da nasarar da aka samu a yi masa aiki a kafarsa a Qatar, in ji mataimakin shugaban asibitin a jiya Lahadi.

Kulob din Neymar na Paris Saint-Germain ya ce kafin a yi masa tiyata a ranar Juma’a, cewa dan wasan mai shekaru 31 zai yi jinyar watanni hudu, wanda hakan ya sa ba zai buga sauran kakar wasa ta bana ba.

Mataimakin darakta janar na asibitin Aspetar Hakim Chalabi kuma tsohon daraktan kula da lafiya na PSG ya shaidawa AFP cewa: “An yi wa Neymar Junior tiyata a jiya, an samu nasara sosai.”

Neymar zai yi kwana biyu a asibitin wasanni na Aspetar da ke Qatar. Bayan hutun lokaci, PSG za ta fara aikin jiyya, in ji Chalabi.

Neymar dan wasan PSG a Faransa
Neymar dan wasan PSG a Faransa AP – Francois Mori

 

“Daga baya za mu tantance lokacin dawowa filin. Yanzun nan ba da jimawa ba za a yi magana.” Ma’aikatan lafiya na kulob din za su tuntubi likitocin bayan an kara duba lafiyarsa.

Neymar ya ji rauni a wasan da suka yi da Lille a gasar Ligue 1 a watan jiya. Ya samu rauni a idon sawu daya a shekarar 2018.

Chalabi ya ce bayan tiyatar, Neymar “ya kamata ya dawo kamar yadda aka saba amma tare da rage hadarin rauni.”

Kula da lafiyar dan wasan ya kasance abin damuwa na yau da kullun tun lokacin da PSG ta sayi Neymar kan Euro miliyan 222 ($ 264m) a cikin 2017.

Ya buga wasanni 112 kacal daga cikin 228 da PSG ta buga a gasar Ligue 1 tun vayan zuwansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here