Gobara ta tashi a kasuwar Singer a Kano

0
189

An wayi garin ranar Litinin da gobara a Kasuwar Singer, wadda ta shahara wajen sayar da kayan abinci a Jihar Kano.

Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta tashi be a cikin tsakar dare kuma har zuwa wayewar garin Litinin ba a gana shawo kan wutar ba.

Jami’an kashe gobara na kokarin shawo kan wutar wadda hotuna suka nuna yadda take ci gaba da ci a sassan kasuwar.

Wasu daga cikin ’yan kasuwar na kokarin kwashe abin da za su iya na daga dukiyarsu da ya rage a Kasuwar Singer.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here