‘Yan bindiga sun kashe mutane 17 a Kaduna

0
61

Akalla mutane 17 ‘yan bindiga suka kashe, yayin wani hari da suka kai kan kauyen Unguwar Wakili da ke yankin karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.

A baya dai rahotannin suka fara fita cewa suka yi mutane 15 suka rasa rayukansu a harin ‘yan ta’addan, amma daga baya mutane biyu daga cikin ukun da suka jikkata suka mutu, abinda ya sa adadin mamatan kaiwa 17.

Bayanai daga wasu majiyoyi sun ce akasarin wadanda ‘yan bindigar suka kashe mata ne da kananan yara, cikinsu har da wata mata da jaririnta.

Yayin zanta wa da manema labarai, shugaban karamar hukumar ta Zangon Kataf Francis Sani ya ce, ‘yan bindigar sun afka wa kauyen na Ungwar Wakili ne da misalin karfe 9 na daren ranar Asabar, nan take kuma suka bude wuta kan jama’a, yayin da suka jikkata wasu da wukake, inda suka shafe sa’o’i suna tafka ta’asar.

Tuni dai aka kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a kauyen na Unguwan Wakili, da sauran yankunan da ke kusa da suka hada da Mabuhu, Zangon Urban da kuma Unguwan Juju, domin baiwa sojoji damar maido da tsaro a yankunan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here