Morocco ta gayyaci Hakimi duk da zargin fyade da ya ke fuskanta

0
110

Duk da zarginsa da ake da laifin aikata fydae a Faransa, Achraf Hakimi ya samu gayyata daga hukumar kwallon kafar Morocco don fafatawa a wasannin sada zumunta da tawagar kwallon kafar kasar za ta yi da kasashen Brazil da Peru.

Mai horar da ‘yan wasan babbar tawagar   kwallon kafar Morocco, Walid Regragui ya ce kasar na goyon bayan dan wasan bayan na Paris Saint Germain, inda ya shaida wa wani taron   manema labarai cewa dole sai an tabbatar a laifin a kansa za a dauke shi a matsayin mai laifi.

Ana tuhumar Hakimi da yi wa wata mata mai shekaru 24 fyade a gidanta, kamar yadda ta shigar da korafi a gaban hukuma, sai dai lauyansa ya ce ana kokari ne a tatsi dan wasan, ta hanyar raba shi da ‘yan kudadensa.

Duk da wannan shari’a  da ake, an bai wa Hakimi dama ya fita wajen Faransa, inda ya buga wa PSG wasan da ta fafata da Bayern Munich.

Regragui ya ce ya tattauna da Hakimi, kuma ya  lura dan wasan bai daga hankalinsa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here