NLC na shirin shiga yajin aiki kan karancin man fetur da takardun kudi

0
85

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga gwamnatin tarayya domin magance matsalar karancin man fetur da Naira da ake fama da shi a kasar nan.

Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana haka a lokacin da yake zanta wa da manema labarai a gidan ma’aikata kan sakamakon taron da kwamitin majalisar ya kira.

Ya ce kungiyar za ta ayyana yajin aikin a fadin kasar nan, tare da daukar kwararan matakai matukar ba a magance manyan matsalolin guda biyu ba bayan kwanaki bakwai.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kotun koli ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin N500 da kuma N1000.

Sai dai shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ya kamata CBN da Ministan Shari’a su martaba hukuncin kotun kolin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here