Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa da Kasa (MNJTF) sun yi nasarar kama mayakan Boko Haram da ISWAP 900 tare da iyalansu da masu taimaka musu a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Rundunar ta kuma ce dakarunta na shiyya ta daya da kuma ta biyu ne suka sami nasarar a kan ’yan ta’addan.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin MNJTF da ke N’Djamena a kasar Chadi, Laftanar Kanal Kamarudeen Adegoke ya fitar ranar Laraba.
Ya ce fadan cikin gidan da ake fama da shi tsakanin Boko Haram da ISWAP, da kuma hare-haren rundunar sun taimaka sosai wajen cafke mayakan
Laftanar Kanal Kamarudeen ya kuma ce a cikin wata dayan da ya gabata, mutane sun rika yin tururuwa daga dajin Sambisa zuwa yankin Tafkin Chadi.
Ya ce, “Ayyukan gamayyar rundunar na shiyya ta uku da ta hudu da ke tafkin Komadugu Yobe, a kan iyakar Najeriya da Nijar, sun yi sanadiyyar kama mutum 900, wadanda suka hada da mayaka da mata da kananan yara da kuma tsofaffi daga cikin ’yan ta’adda.
“Yanzu haka muna ci gaba da aikin hada gwiwa tsakanin kasashe wajen kama wadannan mutanen.
Kazalika, dakarun sun gabatar da sintiri a kan hanyar Ngagam-Djalori, inda suke ceto mata hudu da yaransu biyu, wadanda ke kokarin guduwa daga fadan cikin gida tsakanin Boko Haram da ISWAP a dajin Sambisa,” in ji shi.