Za mu kammala cire tallafin mai kafin zuwan sabuwar gwamnati- Ministar kudi

0
116

Gwamnatin Najeriya ta ce ta na shirin kammala cire tallafin man fetur kafin mika mulki ga sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara.

Ministar kudi da tsare tsaren kasar Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana shirin a Abuja, inda ta ke cewa shirin cire tallafin shi ne wanda jama’a basa so amma kuma ya zama wajibi, a dai dai lokacin da akasarin ‘yan Najeriya suka yarda cewar tallafin baya taimakon talaka.

Ahmed ta ce sun samu umurnin cire tallafin nan da watan Yuni na wannan shekara kamar yadda majalisa ta amince da shi a cikin kasafin kudin wannan shekara, kuma za su aiwatar da shi domin bai wa kasuwa damar samar da farashin a koda yaushe.

Zainab Ahmed ta ce kawo karshen zuba tallafin man zai bai wa gwamnati damar karkata kudin da ake sanyawa zuwa bangarori da dama da suka hada da inganta asibitoci da makarantu da kuma samar da kayan more rayuwa.

Ministar ta bukaci ‘yan Najeriya da su goyawa gwamnatin baya wajen ganin an kawo karshen wannan tallafi wanda ke amfana wasu mutane ‘yan kadan.

Ministar ta ce idan an cire tallafin, zai ba iwa ‘yan kasuwa da masu zuba jari damar shiga harkokin kasuwancin man da kuma samar da shi ga jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here