DSS ta kama wasu mutane a Kano kan zargin tayar da rikici

0
53

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce ta kama wasu mutane biyu da take zargi da tunzura mutane domin tayar da hankali a jihar Kano gabanin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisun jiha da za a yi a ranar Asabar.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter hukumar ta DSS ta ce mutanen sun naɗi hoton bidiyo ne da suke bayanan tunzura jama’a a cikinsu, sannan suka riƙa wallafa shi a shafukan sada zumunta.

Ta kuma wallafa sunayen Sharu Abubakar Taɓule mai shekara 37 a duniya, da kuma Isma’il Iliyasu Mnagu mai shekara 51 a matsayin waɗanda ta kama.

“Cikin waɗannan saƙonnin masu haɗari, sun nuna jam’iyyar siyasar da suke goyon baya kuma suka yi kira ga magoya bayansu su kai wa abokan hamayyarsu hari duk inda suka gansu.

“Waɗanda ake zargin sun yi kira da a kai wa jami’an tsaro hari yayin zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi da za a yi a ranar Asabar.

“Wata jam’iyyar siyasa a Kano na barazanar shirya zanga-zanga a sakamakon shirin kai hare-haren,” in ji hukumar ta DSS.

Sanarwar ta ƙara da cewa jam’iyyar siyasar ta shirya kutsawa ofisoshin wasu hukumomin tsaro a ranar 16 ga watan Maris a matsayin nuna goyon baya ga waɗanda ake zargin.

“Yayin da hukumar ke sanar da mutane kan wannan haramtaccen mataki, ta kuma yi kira ga jam’iyyar da ta dakatar da wannan lamari, ko kuma ta shirya yaba wa aya zaƙinta.

“DSS ba za ta zuba ido tana kallon mutane suna tunzura al’umma ba su tayar da hankali da rashin tsaro a jiha ba.”

Sanarwar DSS ta ce za ta haɗa hannu da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da an samar da cikakken tsaron da zai bayar da damar da gudanar da zaɓe mai inganci a jihar.

Baya ga Kano hukumar tsaron ta kama wasu mutane da ke irin wannan kiraye-kiraye a wasu jihohi a faɗin ƙasar.

Hukumar ta shawarci jam’iyyun siyasa a fadin Najeriya da su gargadi mabiyansu su zama masu bin doka da oda, domin tabbatar da dimokuraɗiyya ta samu wurin zama yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here