Hukumar DSS ce abokiyar hamayyar mu a jihar Kano ba APC ba – NNPP

0
107

Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta yi zargin cewa, babbar abokiyar hamayyarta a jihar ita ce, hukumar jami’an tsaro ta farin kaya DSS ba Jam’iyyar APC ba a zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi a ranar 18 ga watan Maris a jihar.

NNPP ta yi zargin cewa, DSS ta hada kai da APC a Kano don a danne wa mutane ‘yancin su.

Da yake yin magana a madadin NNPP,  dan takarar sanata a jam’iyyar Baffa Bichi ya ce, magoya bayan NNPP za su gudanar da zanga-zanga ta lumana a cikin jihar akan ci gaba da aikin da shugaban DSS Yusuf Bichi ke yi a jihar wanda ya kamata a yi masa ritaya watanni 15 da suka wuce.

Ya ce, zanga-zangar ce kawai mafita ga jam’iyyar ganin cewa, binciken da NNPP ta yi, ta gano cewa, gwamnatin APC ta bar  shugaban DSS ne ya ci gaba da zama akan kujerarsa don ya taimaka wa APC a zaben da ke tafe a jihar.

NNPP ta kuma yi zargin cewa, an turo wasu kwararrun jami’an DSS daga Abuja, inda aka kama masu dakuna a otel don APC ta yi magudin zabe a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here