ISWAP da IPOB na cikin kungiyoyin ta’addanci 10 mafiya hadari a duniya – Rahoto

0
96

Kungiyoyin ISWAP, Boko Haram da kuma IPOB mai taratsin neman ballewa daga Najeriya sun shiga jerin kungiyoyin ta’addanci 10 mafiya hadari a duniya.

Tun a shekarar 2009 Boko Haram ta fara kai hare-hare a Najeriya, tana kuma kara kaimi wajen ayyukan ta’addancin da ya ya ajalin dubban daruwan mutane da kuma sanya wasu miliyoyi gudun hijira.

Daga bisani a wuraren shekarar 2016 kungiyar ta rabe gida biyu, inda mayakanta da suka balle suka kafa kungiyar ISWAP, wadda ita ma ta ci gaba da ayyukan uwarta da sabon salo.

Ita kuwa IPOB me neman ballewa daga Najeriya, a shekarar 2017 Gwamnatin Tarayya ta ayyana ta a matsayin kungiyar ’yan ta’adda, saboda ayyukanta na tashin hankali.

Wani rahoton Alkaluman Ayyukan Ta’addanci a Duniya (GTI) na 2023 ya bayyana cewa kungiyar ta  fi yin barna a shekarar 2023, inda ta kai hare-hare 40, tare da  kashe akalla mutum 57.

Kashe-kashen sun hada da na wasu ma’aurata sojoji da kungiyar ta fille wa kai, da na sauran wasu jami’an tsaro gami da ’yan Arewa da wasu ’yan yankin Kudu maso Gabas da kungiyar ta kashe a shekarar.

Rahoton, wanda Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki da Zaman Lafiya (IEP) ta fitar, ya jaddada matukar hadarin IPOB.

Jerin kungiyoyin da suka fi hadari a duniya su ne:

  1. Kungiyar ta zo ta farko wajen hadari a duniya ita ce IS, wadda ta kashe mutum 1,045 a hare-hare 410 a shekarar.
  2. Al- Shabaab kashe-kashe 784 a har 315
  3. Islamic State – Khorasan Province (ISK) ta kashe mutum 498 a hare-ahre 141
  4. Jamaat Nusrat Al-Islam wal Muslimeen (JNIM), ta kashe mutum 279 a hare-hare 77
  5. Balochistan Liberation Army (BLA), ta kashe mutum 233 a hare-hare 30.
  6. ISWAP ta kashe mutum 219 a hare-hare 65.
  7. Boko Haram ta kashe 204 a hare-hare 64.
  8. Tehrik-e-Taliban Pakistan (TTP) ta kashe 137 a hare-hare 90
  9. Islamic State – Sinai Province ta kshe 71 a hare-hare 27.
  10. IPOB, ta kashe mutum 57 a hare-hare 40.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here