INEC ta ce ba a kammala zabe a jihar Adamawa ba

0
99

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta ayyana zaben gwamnan jihar Adamawa a matsayin wanda ba a kammala ba.

Baturen zabe na INEC a jihar ta Adamawa, wanda ya bayyana hakan a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Yola, ya ce akwai bukatar sake gudanar da zabe a wasu mazabun.

Ya ce, ba za a ayyana wanda ya ci zabe ba, har sai an gudanar da zabe a wasu mazabu 47 daban-daban da ke kananan hukumomin jihar 21.

Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP na kan gaba da yawan kuri’u, inda Sanata Aisha Binani ta jam’iyya mai mulkin kasar wato APC ke biye masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here