Wata tsohuwa ta babbake dan ta da Iyalan sa

0
133

Ana zargin wata tsohuwa mai shekaru 75 ta cinna wa danta, jikokinta biyu da kuma surukarta wuta a Jihar Ondo.

Ana zargin dattijuwar ta yi ajalin dan nata da iyalansa ne bayan ta watsa musu fetur sannan ta cinna musu wuta a cikin gidansu, lamarin da ya haddasa mummunar gobara.

An kai magidancin da iyalan nasa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Owo, inda likitoci suka tabbatar cewa shi da matarsa da daya daga cikin yaran sun rasu.

“Babban dan ne kadai ya rayu, shi ma din a yanzu haka yana cikin mawuyacin hali,” in ji shaidar

[contact-form][contact-field label=”Name” type=”name” required=”true” /][contact-field label=”Email” type=”email” required=”true” /][contact-field label=”Website” type=”url” /][contact-field label=”Message” type=”textarea” /][/contact-form]

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here