Akwai yiwuwar fari ya kashe mutum dubu arba’in da uku 43,000 a bana – Rahoto

0
65

Sama da mutum 43, 000 ne ake fargabar cewa sun rasu a Somaliya a bara bayan rashin samun ruwan sama, kamar yadda sabon rahoton gwamnatin Somaliya da Majalisar Dinkin Duniya ya nuna.

Wannan ne alkaluman da aka fitar a hukumance sakamakon fari daga ƙasar a yankin kusurwar Afirka.

Ana kyautata zaton cewa rabin waɗanda farin ya shafa yara ne ‘yan ƙasa da shekara biyar.

Har yanzu ana fama da matsalar ta fari, inda ake sa ran mutum 18,000-34,000 za su iya rasa rayuwarsu a farkon watanni shida na wannan shekara.

A 2011, matsalar fari da aka fuskanta, ta kashe mutum sama da rabin miliyan.

“Muna iyaƙar kokari wajen ganin mun kare rayuwar mutane,” in ji Dakta Mamunur Rahman Malik, wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya.

Ya ƙara da cewa rashin kawo agaji a kan lokaci, na nufin yara da mata da kuma marasa galihu za su iya rasa ransu, kamar yadda ya faru a baya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bukatar $2.6bn domin taimakawa shirinta na bayar da agaji a Somaliya a wannan shekara. Zuwa yanzu, an samu kashi 15 na kuɗaɗe da ake bukata.

Mummunar farin ta yi sanadiyyar mutuwar dabbobi da kuma amfanin gona da yawa, a farin da sauyin yanayi da rikicin siyasa da kuma hauhawarar farashin kayan abinci a duniya ya ƙara munana shi.

Matsalar da ake fuskanta a yanzu ita ce ta kai kayan agaji a yankunan da al-Shabab ke iko da su, da ke da alaƙa da kungiyar al-Qaeda.

Al-Shabab ta sha kai munanan hare-hare a Somaliya, wanda abu ne kuma da ke kawo cikas wajen kai kayan agaji.

Sai dai tsauraran dokoki da gwamnatin Amurka ta kafa na ganin kungiyoyin ƴan ta’adda basu ci moriyar kayan agaji ba, ya ƙara janyo matsala wajen kai kayan agaji zuwa ga al’ummomin da ke buƙatar hakan.

Wasu jami’an bayar da agaji sun ce al’ummomin ƙasashen waje, yakin Ukraine ya sanya ba su ba da kulawa ga matsalar ta fari.

A watan Janairu, babban jami’in bayar da agaji na MDD a Somaliya, Adam Abdelmoula, ya ce waɗanda ke bayar da agaji sun mayar da hankalinsu kan yakin Ukraine a yanzu, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

An fitar da rahoton ne a ranar litinin wanda Unicef ​​da WHO suka bayar da shi, bincike kuma da makarantar kula da tsaftar muhalli da kuma magungunan da ke London suka gudanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here