INEC ta yi kuskuren ayyana Abba a matsayin gwamnan Kano – Gawuna

0
60

Mataimakin gwamnan jihar Kano da ke Najeriya kuma ‘dan takarar Jam’iyyar APC a zaben da aka yi ranar Asabar, Dakta Nasir Yusuf Gawuna ya ce, hukumar zabe ta yi kuskure wajen bayyana Abba Kabir a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar sakamakon soke zaben wasu mazabun da aka yi.

Yayin ganawa da manema labarai, Gawuna ya ce yawan akwatunan da aka soke ya kai ace hukumar zabe ta sake gudanar da zabuka a wuraren kafin gabatar da kammalallen sakamako da kuma sanar da wanda ya ci.

Mataimakin gwamnan ya ce lura da yadda hukumar zaben ta bayyana zaben ‘yan majalisun jihar Kano 16 a matsayin wadanda ba su kammala ba, wato ‘inconclusive’ ya dace ace ta dauki wannan mataki a zaben kujerar gwamnan.

Gawuna ya ce suna da yakinin cewar Allah ke bada mulki ga wanda ya so a lokacin da yake so, saboda haka za su bi matakan da suka dace ta fannin shari’a domin neman hakkinsu.

Mataimakin gwamnan ya jinjina wa mutanen Kano akan irin goyan bayan da suka ba shi, yayin da ya bukaci kwantar da hankali da kuma kauce wa daukar doka a hannu.

Shi ma a nasa jawabi, shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai ta kasa Hon. Alhassan Ado Doguwa ya ce dokar zabe ta yi tanadin cewar, idan an soke zabe a wasu mazabun da kan iya shafar kammalalen sakamakon baki daya, ya zama wajibi a koma domin sake gudanar da zabe a wadannan wurare kafin gabatar da kammalallen sakamako.

Doguwa ya dauki lokaci yana fashin baki akan irin kuskuren da hukumar zabe ta yi wajen kauce wa amfani da dokokin zaben da aka yi.

Ita dai hukumar zabe ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da kuri’u sama da miliyan guda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here