Na matsu na sauka daga mulkin Najeriya – Buhari

0
116

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada zakuwar sa na sauka daga karagar mulki, domin komawa mahaifarsa Daura dan ci gaba da rayuwa, bayan kammala wa’adin mulkin shekaru 8.

Buhari wanda ya ce ya na ci gaba da lissafin kwanakin da suka rage masa na zuwa ranar 29 ga watan Mayu da zai mika mulki ga zababben shugaban kasa, yace ya zaku ya sauka daga mulki.

Yayin da yake ban kwana da jakadiyar Amurka Mary Beth Leonard dake barin kasar a fadar shugaban kasa, shugaban yace a shirye yake ya koma gida domin ci gaba da kiwon dabbobin sa guda 300 a Daura.

Buhari ya bayyana farin cikin sa da yadda dimokiradiya ke samun ci gaba a Najeriya, musamman ganin yadda zabukan shugaban kasa da majalisun tarayya suka gudana.

Shugaban yace ‘yan Najeriya sun fahimci damar da suke da ita na zabin abin da suke so da zarar an basu dama ta hanyar gudanar da zabe mai sahihanci, kuma babu wanda ya isa ya tilasta musu abin da basa so.

Buhari wanda yace yayi bakin cikin faduwar wasu mutane a zaben da ya gudana, amma kuma yaji dadin an baiwa jama’a damar zabin abin da suke so ba tare da tirsasawa ba.

Shugaban yace sauyin kudin da aka samu ya hana amfani da kudade wajen sayen kuri’u, duk da kiran da yayi cewar idan an baiwa jama’a kudi su karba amma kuma su zabi abin da suke so.

Buhari ya kuma jinjinawa kansa akan rawar da ya taka wajen zaben saboda yadda ya ki sanya baki ko kuma katsalandan akan yadda aka gudanar da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here