Jirgin sama mallakin gwamnatin Najeriya zai fara jigila kafin rantsar da sabon shugaban kasa – Hadi Sirika

0
143

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana cewa, jirgin sama na kasar nan zai fara gudanar da aikinsa kafin ranar 29 ga watan Mayu 2023.

Hadi, ya sanar da hakan ne a yau Alhamis a taron masu ruwa da tsaki kan fannin sufurin jiragen sama karo na 10 da aka gudanar a babban birnin tarayya, Abuja.

A cewarsa, kararakin kotu ne suka janyo cikas wajen gudanar da ayyukan sabon jirgin saman, inda ya ce an gayyato daukacin masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama masu zaman kansu don su zuba jarinsu a fannin amma suka ki saboda ba su aminta da aikin ba.

Sai dai, ya ce a yanzu ana ci gaba da gwamnatin tarayya ta tattauna wa da mahukuntan jirgin sama na Ethiopian Airlines, inda a yanzu ana ci gaba da tattaunawa, inda ya kara da cewa, a mataki na gaba majalisar zartarwar ta amince da yin hadakar.

Ministan ya ci gaba cewa, nan ba da jimawa, jirgin zai fara zirga-zirga a cikin kasar nan da kuma zuwa ketare kafin nan da zuwa ranar 29 ga watan Mayu.

A cewarsa, sabon jirgin zai taimaka matuka wajen kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya da karasa yawon shakatawa da bude ido da samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar nan da kuma bunkasa fannin aikin noma.

Da yake yin tsokaci kan kudaden da suka makale Hadi ya ce, gwamnatin tarayya ta dauki dukkan matakan da suka dace don ganin ba ta kara gazawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here