Sarkin Kano ya taya Abba Kabir murnar lashe zaben gwamnan Kano

0
305

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya taya Abba Kabir murnar lashe zaben gwamnan Kano.

Cikin wata sanarwa daga Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa ta bayyana cewa al’ummar kasar nan sun karbi tsarin mulkin damokaradiyya da matuqar muhimmacin idan akayi la’akari da yadda suka futo domin jefa kuri’unsu kamar yadda tsarin mulki ya bada dama.

Sanawar ta kuma godewa malamai da Limamai da sauran Al’umma bisa addu’ar zaman lafiya da suka dunga yi kafin da kuma bayan gudanar da zaben.

Daga nan fadar Masarautar ta Kano tayi nasiha tare da kira ga sabon gwamnan daya hada kai da dukkanin rukunin al’umma wajen tafiyar da gwamnati, domin yin hakan zai taimaka wajen kyautata rayuwar al’umma da kuma kawo cigaban da ake bukata domin bunkasar tattalin arziki ga jihar Kano da kasa baki daya.

Alhaji Aminu Ado Bayero yayi fatan dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano har ma da sauran sassan kasar nan.

yayi addu’ar fatan kammala tenure mulkinsa lafiya tareda samun cigaban gwamnatinsa da habaka tattalin arzikin jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here