Bidiyon ɓullar baƙin halittu a Katsina ba gaskiya ba ne — Ƴan sanda

0
123

Rundunar ƴansanda a jihar Katsina ta ƙaryata wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo da ke nuna yadda wasu baƙin halittu su ka mamaye Katsina.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Gambo Isah ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a jiya Litinin a Katsina.

“An jawo hankalin rundunar ƴansanda ta jihar Katsina kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo da ke nuna yadda wasu baƙin halittu suka mamaye Katsina.

“Hukumar tana so ta bayyana ƙarara cewa abubuwan da ke cikin bidiyon gaba daya na bogi ne.

“Wannan wani yunkuri ne na kawo naƙasu ga zaman lafiya da mutanen jihar ke samu ta hanyar wani mummunan hali,” in ji Mista Isah, mai muƙamin Sufeto.

Don haka kakakin ya bukaci jama’a da kada su firgita, su yi watsi da faifan bidiyon a matsayin shirin gizo ne kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here