Matsayin azumi ga masu aikin ƙarfi a Ramadan

0
75

Azumi lokaci ne da Musulmai ke kasancewa, ba ci, ba sha, ga kuma ƙauracewa iyali tun daga fitowar Alfijir har zuwa faɗuwar rana.

Mafi yawan lokuta, ana gudanar da ibadar azumin watan Ramadan ne a ƙasashe kamar Najeriya lokacin tsananin zafi.

Mutane a wani lokaci sukan taƙaita wasu ayyuka da ke buƙatar ƙarfi a cikin zafin rana, don ririta kuzarinsu da gudun suƙewa.

Sai dai, yanayin rayuwa kan sa wasu Musulmai su haɗa azumi da aikin ƙarfi kuma a cikin zafin rana saboda yanayin sana’arsu.

Ayyuka kamar faskare da birkilanci da haƙar rijiya da fasa dutse da dako da leburanci suna buƙatar amfani da ƙarfi.

To ko mene ne matsayin azumin masu aikin ƙarfi da Ramadana?

BBC ta tuntuɓi malamai domin jin fahimtarsu a kan wannan batu.

 Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu, Babban Limamin Masallacin Dutse a jihar Jigawa ya ce azumi ya wajaba a kan dukkan musulmi baligi – namiji ko mace.

Dr Abubakar ya ce Al Qur’ani ya ambaci marasa lafiya da aka yi wa uzuri a azumin Ramadana ko matafiyi, “ya wajaba a kansa ya yi lissafin kwanakin da ya ajiye azumi domin larura ko uzuri, ya mayar da azumin a wasu kwanakin bayan wucewar ramadan.”

Malamin ya ƙara da cewa azumi yana da alaka da iko da ƙudura, shi ya sa “waɗanda suke iya yin azumin amma da wahala, su ma idan ba za su iya ba, to sai su ciyar.

Ana nufin mutanen da suke tsofaffi, ko waɗanda suke da cuta, wadda take dawwamammiya ko wadda ba a san maganinta ba, to su ma, sai aka haɗa su da waɗanda suke tsoffi – to kullum sai su ciyar a madadin azumi.”

Babban Limamin na Masallacin Dutse ya bayyana cewa tun da azumi yana da alaƙa da iko da uzuri kuma duk mai uzuri, an ba shi damar daga baya ya rama, malamai sun ambata cewa “idan mutum yana aiki mai wahala kuma aikin nan ba zai iya haɗuwa da azumin ba,

“Kuma ya bi matakai na ya canza aiki, amma bai samu canji ba, sannan ba za a ba shi izini ba, ga shi kuma ba shi ne ke iko da kansa ba – ta yadda zai iya sauya jadawali ya koma aikin dare, duka saboda wannan, to zai iya ajiye azumi.

‘Ya wajaba kullum ya tashi da niyyar azumi’

Amma ba fitowa fili zai yi ya ce ni aikina na wahala ne, don haka ya kwana da niyyar gobe ba zai yi azumi ba, ba a yin haka.” in ji Malamin.

Ya ce dole ne ya tashi da niyyar azumi a matsayinsa na Musulmi lafiyayye mai ƙarfi.

 “Idan yana cikin aikin sai ya galabaita, ya ji ba zai iya ci gaba da azumi ba, to sai ya ci abin da zai tafiyar da rayuwarsa, kuma ya ci gaba da aiki amma kuma zai kame baki, ba ajiye azumin zai yi gaba ɗaya ba.

To sai daga bisani, bayan wucewar azumin Ramadan sai ya rama.”

Ya yi ƙarin haske da cewa “ashe kenan abin da zai riƙe masa rayuwa, yadda ba zai galabaita ya mutu ba, shi ake nema ya ci, idan ya gama wannan sai ya ci gaba da aikinsa.”

A cewarsa, dalilin da ya sa malamai suka ambaci cewa ba zai iya fita ba da niyyar azumi ba, wato mutum ya ce ba zai yi azumi ba saboda aikinsa mai wahala ne, hakan na nufin ya yi asarar azumi.

Don haka aka buƙaci ya fito da niyyar azumi,”

“Idan har ya ci gaba da aikin, kuma ya ji zai iya jurewa, saboda malamai sun ce wannan hukunci ne na abin da ke wahalar da wani, amma mai yiwuwa yana da sauƙi ga wani.

Don haka ba a bayar da hukuncin bai ɗaya ga wannan mas’ala ba, ana barin ta ne a buɗe – duk wanda ba zai iya ba, shi ya san kansa.”

“Sai ya yi ƙoƙari zuciyarsa tana son azumi, tana girmama watan Ramadan ba kawai ya zo yana murna cewa ai malamai sun ba shi fatawa don haka ma shi aikinsa tun da mai wahala ne, an ɗauke masa azumi ba.”

“Azumi yana nan a farilla, kuma idan aka samu uzurin da zai sa a sha ruwa, to daga baya sai an rama shi.” kamar yadda Dr Abubakar Birnin Kudu ya shaida.

Shi kuwa Mallam Muhammad Muhammad Albani Misau da ke jihar Bauchi ya ce son samu ne idan har mutum na da hali, ya yi azuminsa sannan ya mayar da ayyukansa zuwa dare.

Ya ce fahimtar malamai ita ce ga masu irin waɗannan sana’o’i, “su yi aikinsu daidai gwargwado a watan Ramadan da rana, ta yadda ba zai wahalar da su ba, idan kuma suna ganin akwai wahala a ciki, su jinkirta ayyukan nasu su bar su zuwa dare.”

Mallam Muhammad wanda limamin Masallacin Juma’a na Babbar Sakandiren Misau ne ya ce kuskure ne mutum ya ce aikinsa yana galabatarwa don haka ba zai iya azumi ba.

“A ƙa’ida azumin watan Ramadan, wajibi ne a kan kowanne Musulmi, abin da malaman fiqhu suke magana a kai shi ne, idan mutum yana aikin wahala mai tsanani, to zai sha azumi,”

“Ƙa’idar da suke faɗa ita ce sai idan mutum ya zamana cewa ya wahala har ta kai yana suma saboda azumin da yake yi.

Saboda wannan, sai a ce ya sha azumi, amma wanda ba ya yin wannan – za ka je ka yi aikinka, ka je ka huta, ka ce kana shan wahala, ba ka kai wannan matsayin ba,”

“Ba ya halatta mutum ya sha azumi, kuma duk wanda ya yi hakan, to kaffara tahau kansa.

A ƙa’idar abin da suka faɗa (malamai) sai mutum yana cikin wahala mai tsanani sosai, wadda ta kai matsayin da yana faɗuwa magashiyan, to wannan shi ne za a ce ya sha azumi, bayan Ramadan sai ya biya.” in ji malamin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here