Yawanmu ya kai mu ƙwace Majalisar Wakilai a hannun APC – ‘Yan adawa

0
111

Zaɓaɓɓun ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyun adawa a Najeriya, suna da yawan da za su iya ƙwace shugabancin majalisa ta 10, da za a buɗe cikin watan Yuni, a cewar wani ɗan majalisar wakilai na jam’iyyar NNPP.

Wannan matsayi ya fito fili ne bayan wani taro da zaɓaɓɓun ‘yan majalisar wakilan, waɗanda suka fito daga jam’iyyun adawa suka yi a daren Talata.

Matuƙar hakan ta tabbata, matakin zai kasance karon farko tun bayan dawowar Najeriya kan tafarkin dimokraɗiyya a 1999, da ‘yan adawa suka shugabanci wata majalisar tarayyar a ƙasar.

Haɗakar jam’iyyun adawa na PDP da LP da NNPP da APGA da ADC da SDP da kuma YPP suna da adadin kujera 164 a zauren majalisar wakilai bayan zaɓen 25 ga watan Fabrairu.

Yayin da jam’iyya mai mulki ta APC ke da adadin kujeru guda 162.

Masu sharhi na cewa matuƙar ‘yan adawar suka haɗa ƙarfi da ƙarfe, suna da yawan da za su iya shugabantar majalisa ta 10, a ƙalla kafin a ƙarasa zaɓen cike giɓi.

Akwai dai ragowar kujera 33, da za a kammala zaɓensu ranar Asabar 15 ga wannan wata na Afrilu.

Wani ɗan majalisar wakilai da aka sake zaɓe zuwa majalisar a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, Kabiru Alhassan Rurum ya ce a siyasa, komai yana iya faruwa. “Amma dai ba mu tattauna (batun) cewa mu karɓi shugabanci ba”.

Duk da yake, komai yana iya faruwa, in ji shi, don kuwa idan mutum ko taron jam’iyyu suna da rinjaye kuma suka amince su zo su yi tafiya tare, ba shakka suna iya neman komai.

  • 2019

Onarabul Rurum ya ce sun yi ganawar ne don taya juna murna a kan nasarar zaɓen da suka yi.

Sannan kuma ko da a cikinsu babu wanda zai nemi shugabancin majalisar, suna iya dunƙulewa su mara baya ga wani ɗan majalisa a tsakanin masu nema daga jam’iyya mai mulki.

“Za mu yi magana da murya ɗaya domin ƙarfafa dimokraɗiyya da kuma inganta zaman lafiya a majalisa ta 10 da za a buɗe”, a cewar Kabiru Rurum.

“Wannan shi ne babban dalilin da ya sa muka yi wannan taro. Ba a zo da maganar a tsaida wane, ko kar a tsaida wane ba”.

Ya nanata cewa sai dai a tsarin irin na siyasa, komai ana iya kawo shi kan teburin tattaunawa, kuma komai yana iya faruwa.

Duk da yake, “Tattaunawarmu ba ta kai matsayin wa za a zaɓa, ko kuma mu a matsayinmu na jam’iyyun hamayya, ko za mu tsayar da wani a matsayin sifika a cikinmu ba. Babu wannan zancen a yanzu”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here