Isra’ila ta ɗora alhakin harin da aka kai mata a kan Lebanon

0
97

Sojojin Isra`ila sun sanar da kama wasu rokokin yaƙi da a ka harbo daga Lebanon guda 25.

Wasunsu sun dura a Isra’ilan kuma sun lalata tituna da ababan hawa.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ce wani mutum guda ya samu rauni kaɗan da harbin bindiga, wasu rahotanni da ba a tantance sahihancin su ba sun ce ƙasar ta mayar da martani ta iyakokinta.

Babu wanda ya ɗauki nauyin kai harin wanda ya afku a lokacin da hankula suke a tashe.

Wani bidiyo ɗauke da yadda ‘yan sanda su ke korar Musulmi ma su Ibada a Masallacin Al-Aqsa ya haifarwa da Isra`ilan martanin hare-hare daga bangarori daban-daban.

Kakakin rundunar sojin Isra`ila ya shaida wa manema labarai cewar kungiyoyin ‘yan bindiga daga Falasdinu da ko Hamas ko ‘yan Jihadi, kuma ana zargin Iran na da hannu.

Firaiminista Benjamin Netanyahu ya jagoranci taron tsaro da majalisar zartaswar kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here