‘Yan mata 20,000 da aka aurar bara sun haifi jarirai 10,000 a Iran

0
78

Yan mata fiye da 20,000 ne ‘yan shekara 15, aka yi wa aure a cikin wata taran da ya gabata a ƙasar Iran, a cewar alƙaluman Cibiyar Ƙididdiga ta Ƙasar.

A cewar alƙaluma da jaridar intanet ta Etemad ta wallafa, an kuma samu “sakin aure 179 a cikin ‘yan matan ‘yan ƙasa da shekara 15”.

Akwai ‘yan mata ‘yan ƙasa da shekara 15 da suka haifi jarirai 1,085.

Cibiyar Ƙididdigar ta wallafa wannan rahoto ne a kan halin rayuwar zamantakewa da ta al’adar al’ummar Iran a cikin watanni ukun farkon shekara.

A cewar dokokin kula da hulɗar jama’a na Iran, shekarun aure ga ‘ya mace suna farawa ne daga 13, maza kuma daga shekara 15.

Haka zalika, ana iya aurar da mutum wanda shekarunsa ba su cika ƙa’ida ba, bisa doka amma da sharaɗin yardar mahaifi ko wani mai kula da shi sannan sai kotu ta amince.

Yunƙurin canza shekarun aure a majalisar dokokin Iran yana da dogon tarihi a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here