Faɗan ƙabilanci ya yi sanadin mace-mace a Taraba

0
114

Ana fargabar cewa mutane da dama ne suka rasu a wani faɗa tsakanin Kuteb da Fulani makiyaya a cikin ƙaaramar hukumar Ussa ta jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa “Duk da yake, ba a san musabbabin rikicin ba, amma wani ganau ya ce ƴan ƙabilar Kuteb ne suka zargi Fulani da kai hari kan mutanensu, abin da ya haddasa kisan kai da kuma yin garkuwa da wasu”.

Ganau ɗin ya ce hakan ta sa ‘yan ƙabilar Kuteb suka kai wa Fulani hari a Kwe Sati, jiya Alhamis, abin da ya sa faɗan ya bazu zuwa garin Fikye in ji shaidan.

Ana kyautata zaton cewa mutane da yawa sun rasu.

Jagoran ƙungiyar al’ummar Kuteb, Emmanuel Ukwen, ya faɗa wa Daily Trust cewa an samu asarar rayuka daga dukkan ɓangarorin kabilun biyu.

Ya ce mutane sun tsere wa yankin yayin da ake ci gaba da faɗa, inda kuma aka ƙona gidaje da dama.

Rahotanni sun ce an kai hari gidan Sarkin Lisam Kwe, Ando Madugu, inda wasu fusatattun matasa suka ƙona fadarsa bayan sun zarge shi da mara wa Fulani baya.

A cikin makon nan ne, shugaban ƙaramar hukumar ta Ussa, Abershi Musa, ya yi murabus, bayan ya zargi gwamnatin jihar da kasa ɗaukar mataki a kan kashe-kashen mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, da ya zargi Fulani da yi.

Lokacin da aka tuntuɓi shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na ƙaramar hukumar, Alhaji Bello, ya ce ba zai yi magana kan lamarin ba a halin yanzu.

Shi ma, mai magana da yawun ƴan sandan jihar, SP Usman Abdullahi, ba a same shi ba lokacin da aka kira wayarsa don ji daga gare shi game da wannan al’amari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here