Bayan umarnin kotu an yanka zakaran nan mai cara

0
124

Magidancin nan Isyaku Shu’aibu da maƙocinsa ya yi ƙararsa a Kotu kan yawan Carar Zakaransa ya yanka abinsa ranar Jumu’a don biyayya ga umarnin Kotu.

Idan baku manta ba kwanakin baya ne Kotun Majistiri da ke gidan Murtala a Kano ta umarci wani mutum Isyaku Shu’aibu da ke unguwar Ja’en ya yanka Zakaransa bisa karar da makwabcinsa ya kai kotu kan damunsa da zakaran yake da cara cikin dare.

Maƙocinsa Malam Yusuf Muhammad Ja’en ne ya shigar da ƙara Kotun kan cewa Zakaran yana shiga haƙƙinsa ta hanyar hana shi barci da yawan Cara.

Amma koda aka karantowa wanda ake ƙara ya ce, gaskiya ne Zakaran na yawan yin Cara kuma zai yanka shi ne a bikin “Good Friday” don haka ya roƙi Kotun da ta sahale masa zuwa ranar.

Malam Isyaku ya shaidawa filin INDA Ranka cewa sun sha dabgen zakaran da iyalansa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here