Rahoton UNICEF ya jefa wasu ‘yan Nijar cikin fargaba

0
75

Wasu al’ummar Jamhuriyar Nijar sun bayyana fargabarsu game da gargadin da Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya yi kan yiwuwar mutuwar yara sakamakon rashin tsaftataccen ruwan sha.

A wani sabon rahoto da ya fitar ranar Laraba don bikin Ranar Ruwa ta Duniya, UNICEF ya ce akalla yara miliyan 190 a kasashen Afirka 10 ka iya mutuwa sakamokon rashin tsaftataccen ruwan sha.

Rahoton ya bayyana cewa yaran na iya fuskantar manyan hadura uku masu alaka da ruwa da suka hada da rashin wadataccen ruwa, da rashin tsaftar jiki da muhalli da kuma tasirin sauyin yanayi. Kasashen 10 da asusun ya ambata sun hada da Jamhuriyyar Nijar da Benin da Burkina Faso da Kamaru da Chadi da Cote d’Ivoire da Guinea da Mali da Nijeriya da kuma Somaliya.

Binciken ya kara da cewa yawancin yaran da lamarin zai fi shafa a yankin kasashen Sahel da ya jima yana fama da matsalar tsaro ne, wanda kuma ake ganin zai yi tasiri wajen ta’azzara matsalar karancin ruwan sha da na tsaftace muhalli ga yara.

Wasu al’ummar Jamhuriyyar Nijar da TRT Afrika ta tattauna da su sun bayyana yadda matsalar rashin tsaftataccen ruwa ke addabar su, da irin mummunan tasirin da hakan ke yi a kan yara.

Wata mata mazauniyar garin Dosso, Larba Dauda, ta shaida wa TRT Afirka cewa rahoton ya girgiza ta musamman ganin cewa suna fama da karancin ruwa mai tsafta.

“Kusan duk shekara sai an samu annoba – babba ko karama – a wannan yanki da za take ajalin yara saboda rashin tsaftaccen ruwan sha da rashin kula da muhallanmu da shi. “Dole wannan sabon labari ya daga wa iyaye hankali, amma muna fatan hukumomi su kawo dauki mataki na gaggawa kan lamarin,” in ji Larba Dauda.

Abdou Dan Naito, wani magidanci mazaunin birnin Maradi, ya shaida wa TRT Afirka matsalar rashin ruwa mai tsafta ta dade tana addabarsu. Ya kara da cewa duk da yake a yanzu ana samun ci gaba wajen samar da ruwan sha a kauyuka da birane amma “har yanzu da sauran rina a kaba don kuwa a wasu lokutan akan shafe makonni ba a samu ruwa mai tsafta sosai ba.

“Don haka mutane ba su da zabi sai shan na rafi ko koramu da ba su da cikakkiyar tsafta”, in ji shi.

Amma kuma ya yaba wa gwamnatin kasar game da yadda take kokarin gina rijiyoyin burtsatse a yankuna da dama a fadin kasar. Nijar ta sha fama da matsaloli daban-daban da suka shafi rashin isasshe da tsaftataccen ruwan sha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here