Takardun sirri, da sojojin Amurka suka boye,an falasa su a shafukan sada zumunta,daya daga cikin jaridun kasar ta Amurka , jaridar New York Times ta bayyana haka a ranar alhamis.
WaÉ—annan takarddun sun kunshi adadi masu mahimmanci da bayanai masu alaka da yaÆ™in Ukraine. Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta kaddamar da bincike. Nan da nan wadannan bayyanai sun bazu a cikin da’ira na masu goyon bayan Rasha da kuma kafofin watsa labarun da suka himmatu ga manufar Vladimir Putin. Bayyanai daga hukumar DIA, hukumar leken asirin Soja ta samar, da rabin shafuka goma sha biyu na bayyanan sirri cikin lokaci, waÉ—anda aka sabunta a cikin watan maris, waÉ—anda ke nuna girman goyon bayan Amurka ga Æ™oÆ™arin yaÆ™in Ukraine.
Mun gano, alal misali, jadawalin horo ga dakarun Ukraine ko adadin amfani da harsashi na kasashen waje da aka harba a kan Rasha.
A daya geffen ,an samu Karin haske dangane da adadin sojojin yammacin da aka tura a Ukraine. Kuma musamman, na sojojin na kasashen NATO: 14 daga Amurkawa, 50 daga  Birtaniya, 15 daga Faransa, 17 daga Latvia. Wanda yawan su yak ai dari kenan.
Ana samun karin bayyani dangane da ƙiyasin asarar da sansanonin biyu suka yi. Fiye da sojoji 35,000 suka mutu a bangaren Rasha, dubu 16 zuwa 17,000 sun mutu a bangaren Ukraine: a cewar hukumar leken asiri ta DIA,.
Rasha ta yi asarar sojoji sau biyu fiye da Ukraine. Kungiyoyi  masu goyon bayan Rasha sun yi gaggawar daukar wadanan bayyanai kuma tuni su shiga cikin yadda wadanan bayyanai zuwa sauran shafuka.
Da aka yi mata tambayoyi, ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin. Mai magana da yawun Pentagon Sabrina Singh ta ce “Muna sane da rahotannin manema labarai game da labaran da aka wallafa a shafukan sada zumunta kuma sashen na nazarin lamarin.“