Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun bayyana damuwa kan ƙaruwar fasa-ƙwaurin miyagun ƙwayoyi a tsakanin iyakar ƙasar da Najeriya da kuma Jamhuriyar Benin.
Hakan na zuwa ne bayan da aka kama ɗaruruwan ɗauri na tabar wiwi da wata ƙwaya nau’in baliyam mai hatsari, da aka yi yunƙurin shigarwa ƙasar a ranar Juma’a daga wata ƙasa mai maƙwabtaka.
Shugaban gundumar Gaya a cikin jihar Dosso, kudu maso yammacin Nijar, Ashimu Abarshi ne ya yi wa BBC ƙarin bayani game da kama miyagun ƙwayoyi na baya-bayan nan.
Ya ce ƙwayoyin da suka kama sun haɗar da tabar wiwi ɗauri 400 da kuma ɗauri 1,260 na wata ƙwaya mai suna Diezepam, da kuma ƙarin ɗauri biyar na ganyen wiwi, da aka yiwo fasa-ƙwaurinsu a cikin kwale-kwale ta Kogin Isa.
Jami’in ya ce a baya-bayan nan, ga alama masu fasa-ƙwaurin ƙwayoyi sun ƙara ƙaimi inda suke amfani da hanyoyin sufuri wajen safarar ƙwayar ta cikin Jamhuriyar Nijar.
Ashimu Abarshi bai bayyana ƙasar da suke hasashen za a shigar da ƙwayar daga Nijar ba, amma ya tabbatar da cewa ana fiton kayan laifin ne a tsakanin Jamhuriyar Benin da Nijar da kuma Najeriya.
“Wanga babban kamu, an yi shi ne bakin ruwa. Jami’an kwastam na ruwa sun zagaya da dare….ƙarfe 10:30 na dare, sai suka ci karo da wani kwale-kwale ya ƙetaro ruwa, ya fito daga wata ƙasa ta maƙwabta”, in ji shi.
Ya ƙara da cewa jami’an sun hangi wasu matasa biyu, da suka tsere bayan ganin jami’an hana fasa-ƙwaurin, inda suka zubar da kayan da ake ƙoƙarin yin safararsu.
Shugaban gundumar Gaya, mai nisan kilomita 254 daga Niamey babban birnin Nijar a gaɓar Kogin Isa ko Kwara, ya ce masu safarar ƙwayoyin na amfani da hanyoyin ruwa ne ko motocin bas-bas masu doguwar tafiya, haka kuma suna bin dazuka a kan babura.
“A ‘yan kwanakin ga biyu, safarar miyagun ƙwayoyi ta zama ruwan dare gama duniya a nan gundumarmu ta Gaya. Abin da ya kamata a gane, shi ne muna da iyaka da ƙasa biyu na maƙwabta.
Daga yamma muna da iyaka da Jamhuriyar Benin, daga kudu maso gabas, Jamhuriyar Najeriya”.
A cewarsa, ana safarar ƙwayoyin ne daga ƙasashen masu maƙwabtaka da Nijar, don yin fito zuwa wata ƙasa a cikinsu ko kuma a wasu ƙasashen na daban.
“Ka san waɗannan ƙwayoyi ana ɗauko su ne, ta wasu ƙasashe na Yammacin Afirka, kuma tilas inda za a wucewa da su, sai an biyo ta nan”.
“In ana so a tai ƙasar Najeriya da su dole sai an biyo ta Gaya. In ana a shigo nan Nijer a yi wasu ƙasashe maƙwabta (da su), dole sai an biyo ta Gaya,” in ji Ashimu.