Buhari zai tafi Saudiyya a ziyararsa ta karshe a matsayin shugaban ƙasa

0
101

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai tafi Saudiyya ranar Talata a wata ziyara ta karshe da zai kai wata ƙasar waje a matsayin shugaban ƙasa.

Shugaban zai shafe kusan mako guda daga ranar 11 ga watan Afrilu zuwa 19 ga wata.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar ya fitar, ta ce Muhammadu Buhari zai kuma gudanar da aikin Umrah yayin ziyarar tasa.

Sanarwar Mallam Garba Shehu ta kuma ce Shugaba Buhari zai samu rakiyar manyan mukarraban gwamnatinsa a wannan ziyara zuwa Saudiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here