Isra’ila ta hana Musulmai yin ibada a masallacin Ibrahimi saboda ranar hutu ta Yahudawa

0
52

Isra’ila ta rufe masallacin Ibrahimi da ke birnin Hebron a Yamma da Kogin Jordan inda ta hana Musulmai masu ibada shiga har tsawon kwana biyu, saboda bikin ranar tunawa da samun ‘yancin Yahudawa daga bautar da Misirawa suka yi musu.

Daraktan masallacin Ghassan al Rajabi ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar Turkiyya, Anadolu hakan a ranar Lahadi.

“Sojojin Isra’ila sun rufe Masallacin Ibrahimi da ke birnin Hebron na Yamma da Kogin Jordan amma kuma sun bar ‘yan Isra’ilan shiga wajen.”

Ya ce masallacin zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa ranar Litnin da yamma.

Wani dan gwagwarmaya dan Falasdinu Aref Jaber ya ce sojojin Isra’ila sun kafa shingayen bincike a yankin masallacin, gabanin bikin ranar tunawa da samun’yancin Yahudawa daga hannun Misirawan, wanda ake kira Passover.

Ya ce ana sa ran dubban Isra’ilawa ne daga fadin Yamma da Kogin Jordan za su je masallacin don gudanar da shagalain bikin ranar hutu ta Yahudawan.

Musulmai da Yahudawa duka suna girmama Masallacin Ibrahim da ke Hebron, saboda an yi amanna a can ne aka binne Annabi Ibrahim da Annabi Ishaq da kuma Annabi Yakub.

Bayan wani kisan kiyashi da wani Bayahude mai tsattsauran ra’ayi, Baruch Goldstein ya yi wa Falasdinawa 29 a cikin masallacin a shekarar 1994, sai hukumomin Isra’ila suka raba harabar masallacin tsakanin Musulmai da Yahudawa masu iabda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here